An yi wa gwamnatin Niger Grambawul | Labarai | DW | 01.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi wa gwamnatin Niger Grambawul

Bayan wata da wattani a na jira, a ƙarshe dai, yau ne shugaban ƙasa Tandja Mamadu,na Jamhuriya Niger, yayi garambawul ga gwamnatin sa.

Ministoci 8 su ka shiga wannan sabuwar gwamnati, da ta ƙunshi a jimilce ministoci 31, a maimakon 26 na russasar gwamnatin.

Ministoci 3 a ka fidda, wanda su ka haɗa da Labo Musa, na harakokin noma, da Usman Galadima ministan ilimi mai zurfi da bincike, da kuma Abdu Dauda, ministan bada horon ayyukan hannu.

Daga sabin ministocin da su ka shigo,akwai na cikin gida Albade Abuba, wani na hannun damar shugaban ƙasa, da kuma Isaka Labo, ministan kulla da al´ammuran addini.

Wannan shine karo na farko, da a ka ƙirƙiro gurbin ministan harakokin addini, a Jamhuriya Niger, mai yawan musulmi kimanin kashi 99 bisa 100, na jama´ar ƙasar, su milion 12.