An yi tir ga shirin Isra´ila na tsugunar da yahudawa ´yan kakagida | Labarai | DW | 28.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi tir ga shirin Isra´ila na tsugunar da yahudawa ´yan kakagida

Kasashen KTT da kuma Amirka sun yi suka da kakkausar harshe dangane da shirin gwamnatin Isra´ila na gina sabbin matsugunan Yahudawa a Gabar Yamma da Kogin Jordan. Finnland wadda ke rike da shugabancin majalisar shawara ta kungiyar EU ta bayyana wannan mataki da cewa ya saba da dokoki na kasa da kasa kuma babban cikas ga kokarin da ake yi na samun wata maslaha ta kasashe biyu. Ita kuwa Amirka ta bukaci gwamnatin Isra´ila da ta yi mata bayani ne. Isra´ila na shirin tsugunar da wasu yahudawa ´yan share wuri zauna a wani tsohon sansanin sojin ta dake Gabar Yammacin Kogin Jordan dake karkashin mamayen ta. Wannan mataki ya sabawa ka´idojin shirin wanzar da zaman lafiya tsakanin Isra´ila da Falasdinawa, shirin da Amirka ke goyawa baya.