1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi tir da tone-tonen da Isra´ila ke yi a karkashin Masjid Al-Aqsa

February 10, 2007
https://p.dw.com/p/BuSA

Sarkin Jordan Abdullah na biyu ya yi kira ga Isra´ila da ta daina aikin gine-gine da tone tone da take yi a harabar masallacin Al-Aqsa dake birnin Kudus. Sarkin yayi tir da aikace aikacen da Isra´ila ke yi a haraba da kuma wasu wurare dake karkashin masallacin yana mai cewa hakan ka iya zama wani sabon tarnaki ga shirin samar da zaman lafiya. A jiya an yi artabu tsakanin jami´an tsaron Isra´ila da Falasdinawa masu zanga-zangar nuna adawa da aikin ginin. Su kuwa bangarorin nan 4 dake shawarta batun zaman lafiya yankin GTT fata suka nuna cewar yarjejeniyar da aka cimma game da raba madafun iko tsakanin Falasdinawa zata kawo karshen mummunar zubar da jini da aka shafe watanni ana yi tsakanin kungiyoyin Falasdinawa dake gaba da juna. Bangarorin sun yi maraba da rawar da Saudiya ta taka wajen cimma wannan yarjejeniya.