An yi tir da sanarwar da Blair ya bayar da cewa ba ta wadatar ba | Labarai | DW | 08.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi tir da sanarwar da Blair ya bayar da cewa ba ta wadatar ba

Shugabannin kungiyoyin kwadago a Birtaniya sun soki sanarwar da FM Tony Blair ya bayar cewa zai yi murabus a cikin shekara guda da cewa ko kadan bata wadatar ba. Sakatare janar na kawancen kungiyar kwadago ta TUC, Brendan Barber ya yi gargadi game da shiga wani yanayi mai dorewa na rashin sanin tabbas. Shi kuwa shugaban kungiyar kwadago ta Amicus Derek Simpson cewa ya yi ai tuni FM ya rigaya yayi murabus. Bayan matsin lamba da ya sha daga ´ya´yan jam´iyarsa ta Labour, a jiya alhamis Blair ya sanar da cewa zai sauka daga kan mukamis a cikin shekara daya, to amma ya ki ya fadi takamaimai ranar da zai sauka.