1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi tir da farmakin da jiragen saman yakin Amirka suka auna kan Zawahiri

January 14, 2006
https://p.dw.com/p/BvCM

Dubban wasu ´yan kabila a kasar Pakisan sun gudanar da zanga-zangar yin Allah wadai da wani farmaki da jiragen saman yakin Amirka suka kai, inda suka auna mataimakin shugaban kungiyar al-Qaida. Farmakin dai wanda aka kai a kusa da kan iyakar Pakistan da Afghanistan ya yi sanadiyar mutuwar mutane 18. Wadanda suka shaida abin da ya faru sun ce mutane kimanin dubu 5 suka yi taron gangami a wani filin wasa dake yankin Bajur, inda aka kai harin na jiya juma´a. A halin da ake ciki jami´an Pakistan na gudanar da bincike don gano ko shin an halaka na hannun damar Osama Bin Laden wato Ayman al-Zawahiri a farmakin na jiya. Kafofin yada labarun Amirka sun rawaito wasu jami´an leken asiri na cewa an auna wannan hari ne akan al-Zawahiri. To amma mazauna yankin sun ce dukkan wadanda aka kashe a harin ´yan kabilar yankin ne kuma mata da kananan yara na daga cikin wadanda suka rasa rayukansu.