1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi sabon yunkuri don kawo zaman lafiya a lardin Darfur

August 18, 2006
https://p.dw.com/p/BumO

Kasashen Birtaniya da Amirka sun dauki sabon mataki da nufin samar da zaman lafiya a yankin Darfur mai fama da rikici dake yammacin Sudan. Yanzu haka dai kasashen biyu sun gabatar da sabon daftarin kuduri a gaban kwamitin sulhu. Kudurin ya goyi da bayan kiran da babban sakataren MDD Kofi Annan ya yi na tura sojojin majalisar kimanin dubu 17 zuwa lardin na Darfur don maye gurbin sojojin Kungyiar tarayyar Afirka su dubu 6 da 200. Mataimakin jakadan Amirka a MDD Jackie Sanders ya ce halin da al´umar yankin ke ciki yana kara yin muni. Har dai halin da ake ciki shugaba Omar el-Bashir na adawa da girke sojojin MDD a cikin kasar ta Sudan.