An yi mummunan batakashi tsakanin sojin Isra´ila da Falasdinawa a Gaza | Labarai | DW | 01.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi mummunan batakashi tsakanin sojin Isra´ila da Falasdinawa a Gaza

An yi wani gumurzu mafi muni a Zirin Gaza tun bayan da sojin Isra´ila suka kutsa wannan yanki a ranar laraba da ta gabata. Sojojin sa kai na Islama da sojojin Isra´ila sun gwabza kazami fada a kudanci yankin na Falasdinawa. Mayakan kungiyar Hamas sun harba rokoki akan wata motar sojin Isra´ila. To sai dai babu wani rahoto ko da akwai wadanda suka samu rauni a wannan hari. A kuma halin da ake ciki Isra´ila ta yi watsi da bukatun da sojojin sa kai na Falasdinawa wadanda suka yi garkuwa da wani sojin Isra´ila suka gabatar na a sako firsinonin Falasdinawa dubu daya daga gidajen kurkukun Bani Yahudu kafin su saki sojin Isra´ila da suka yi garkuwa da shi. Rahotanni da gwamnatin Falasdinawa ta bayar sun nunar da cewa sojin na nan da ransa kuma ana yi masa magani sakamakon raunin da ya samu .