An yi maraba da sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a Darfur | Labarai | DW | 06.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi maraba da sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a Darfur

Gamaiyar kasa da kasa ta yi maraba tare da yin fatan alheri game da sanya hannu akan yarjejeniyar wanzar da zaman lafiyar lardin Darfur, dandalin rikici dake yammacin kasar Sudan. Babban sakataren MDD Kofi Annan ya nuna lale da yarjejeniyar wadda gwamnatin birnin Khartoum da babbar kungiyar ´yan tawaye suka rattabwa hannu. A lokaci daya babban sakataren yayi kira ga sauran kananan kungiyoyin ´yan tawaye biyu da su yi amfani da wannan dama ta tarihi kana kuma su amince da yarjejeniyar.

A gobe lahadi idan Allah Ya kaimu babban jami´in dake kula da ayyukan taimakon jin kai na MDD Jan Egeland zai kai ziyara lardin na Darfur don gane wa idonsa halin da ake ciki.