An yi maraba da sakamakon taron kolin kungiyar EU | Labarai | DW | 10.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi maraba da sakamakon taron kolin kungiyar EU

Babban sakataren MDD Ban Ki Moon ya yi maraba da sakamakon taron kolin KTT akan kare muhalli. A cikin wata sanarwa da ya bayar, Ban ya ce kudurin da kungiyar EU ta zartar ya na da burin tallafawa sabbin fasahohi wadanda kasashe masu tasowa zasu iya amfani da su a kokarin su na yaki da sauyin yanayi. A nata bangaren SGJ Angela Merkel cewa ta yi yanzu EU ta zama jagaba a manufofin samar da makamashi da kare muhalli. A karkashin jagorancin ta, shugabannin kasashen kungiyar EU sun amince da wata yarjejeniya wadda ta tanadi rage fid da hayaki mai dumama yanayi da kimanin kashi daya cikin 5 kafin shekara ta 2020 idan aka kwatanta da shekarar 1990. Yarjejeniyar ta kuma tanadi karin samar da makamashi ta amfani da karfin rana, ruwa da iska da misalin kashi 20 cikin 100.