An yi maraba da sabuwar gwamnatin Iraki | Labarai | DW | 20.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi maraba da sabuwar gwamnatin Iraki

default

Kasashen duniya sun yi lale marhabin da kafa sabuwar gwamnatin hadin kan kasar Iraqi. KTT ta bayyana wannan ci-gaba da aka samu da cewa wani abin karfafa guiwa ne ga yunkurin dinke barakar dake tsakanin al´umar Iraqi. Shi kuwa a nasa bangaren babban sakataren MDD Kofi Annan ya yaba ne da labarin da ya samu na kafa sabuwar gwamnati a Iraqi sannan ya yi mika sakon taya murnarsa ga sabbin shugabannin wannan kasa. Wata sanarwa da kakakin sa ya bayar ta nunar da cewa babban sakataren yayi maraba da sanarwar kafa sabuwar gwamnati a Iraqi sannan ya mika sakon fatan alheri ga FM Nuri al-Maliki da sauaran ´ya´yan gwamnatin farko da aka zaba ta hanyar demukiradiya a Iraqin.