1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi maraba da rahoton binciken game da kisan gillar da aka yiwa Rafik Hariri

October 22, 2005
https://p.dw.com/p/BvOL

Dan tsohon FM Libanon da aka yiwa kisan gilla Rafik Hariri, ya yi lale maraba da rahoton MDD wanda ya zargi jami´an leken asirin Syria da hannu a kisan da aka yiwa mahaifin nasa. A lokacin da yake tofa albarkacin bakin sa dangane da rahoton Sa´ad Hariri ya kuma yi kira ga wata kotun kasa da kasa da ta hukunta wadanda suka aikata wannan laifi. A cikin watan fabrairu Rafik Hariri tare da wasu mutane 20 suka rasu a fashewar wani bam a birnin Beirut babban birnin Lebanon. Wani rahoton bincike da aka mikawa MDD ya nuna shaidar cewa Syria da kuma Lebanon na da wata masaniya dangane da kisan. Shugaban Amirka GWB yayi kira ga MDD da ta hanzarta shirya wani taro don nazarin irin martanin da za´a mayar dangane da binciken. A kuma halin da ake ciki Syria ta nuna shirin yin shawarwari tare da ba da cikakken hadin kai ga jami´an binciken na MDD don gano gaskiya a kisan na Hariri. A lokaci daya kuma mataimakin ministan harkokin wajen Syria Ahmed Arnus ya sake yin watsi da zargin da aka yi cewa kasarsa na da hannu a wannan kisa.