1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi maraba da nasarar da taron kolin kungiyar EU ya samu

December 17, 2005
https://p.dw.com/p/BvG5

SGJ Angela Merkel ta bayyana yarjejeniyar da aka cimma akan kasafin kungiyar tarayar Turai da cewa wata alama ce mai karfafa guiwar nahiyar Turai. Merkel ta yi maraba da kasafin kudin wanda ta ce zai rage wani nauyi dake kan Jamus. Shugabar gwamnatin ta Jamus ta kara da cewa yanzu tarayyar Turai ta yi karfi kuma zata samu sukunin tinkarar wasu manyan matsaloli dake gabanta wato kamar ta kundin tsarin mulkinta dake barazanar rugujewa. Shi ma a nasa bangaren FM Birtaniya Tony Blair ya ce inda ba´a cimma daidaito ba da watakila hakan ya shafi dangantaka tsakanin Birtaniya da Jamus. Blair ya fadawa BBC cewa inda an tashi baram baram a taron to da haka ya yi mummunar illa tsakanin London da sabuwar gwamnatinbirnin Berlin. Shi ma FM Poland Mracinkiewic ya yaba da yarjejeniyar wadda ta tanadi karin kudi ga taimakon raya kasa da EU ke ba gwamnati a birnin Warsaw. Shugaban hukumar kungiyar EU Jose Manuel Barroso ya ce yanzu Turai ta doshi hanyar samun gagarumar bunkasa.