1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi maraba da nadamar da Paparoma ya yi

September 16, 2006
https://p.dw.com/p/BujH

Paparoma Benedict na 16 ya yi na dama da cewa kalaman da yayi akan addinin Islama a wajen wata lacca a nan Jamus ya ba ta ran musulmi. A cikin wata sanarwa da sakataren fadar Vatikan Tarcisio Bertone ya bayar, ya ce Paparoma ya yi bakin ciki cewa wani sashe na jawabin da yayi ya matukan bata ran musulmi. Sanarwar ta ci-gaba da cewa Paparoman na mutunta musulmi da addinin Islama, kuma ya na fata za´a fahimci ainihin abin da yake nufi a cikin jawabin na sa. A halin da ake ciki majalisar tsakiya ta musulmin Jamus ta yi lale maraba da wannan sanarwa ta neman gafara, inji shugabanta Ayyub Axel Köhler sannan sai ya kara da cewa.

Ayyub Köhler ya ce:

“Muna farin ciki da wannan sanarwa, kuma ina ganin yanzu dukkanmu gaba ki daya zamu iya fuskantar gaba. Na san al´umar musulmi zasu yi hakuri cikin gaggawa. Zamu yi duk iya kokarin ganin an kwantar da hankali sannan muna fata zamu samar da wani kyakkyawan yanayin fahimtar juna ta hanyar karfafa tuntubar juna.”