An yi maraba da kudurin da kwamitin sulhun MDD ya amince da shi | Labarai | DW | 12.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi maraba da kudurin da kwamitin sulhun MDD ya amince da shi

SGJ Angela Merkel ta yi lale maraba da amincewa da kudurin kwamitin sulhun MDD game da kasar Lebanon. A lokacin da take magana a birnin Berlin Merkel ta ce wannan wani muhimmin mataki ne da gamaiyar kasa da kasa ta dauka da nufin kawo karshen yakin da ake yi tsakanin Isra´ila da kungiyar Hisbollah. Ta ce a kullum gwamnatin Jamus na goyon bayan bin hanyoyin diplomasiya wajen warware wannan rikici. Merkel ta ce abin da ake bukata yanzu shi e a hanzarta aiwatar da kudurin. Shi ma shugaban Faransa Jacques Chirac da FM Birtaniya Tony Blair sun yi kira da a dakatar da yakin nan take.