An yi kira ga Turkiya da ta girmama yarjejeniyar birnin Ankara | Labarai | DW | 07.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi kira ga Turkiya da ta girmama yarjejeniyar birnin Ankara

SGJ Angela Merlkel ta yi gargadin cewa ka da a bari jayyayar da ake akan tsibirin Cyprus ta dagula al´amura a kokarin Turkiya na shiga KTT EU. Merkel ta bayyana haka ne bayan tattaunawar da ta yi da ta yi FM Finland Matti Vanhanen, wanda kasarsa ke rike da shugabancin kungiyar EU. Merkel ta sake nanata cewa dole ne Turkiya ta yi aiki da yarjejeniyar ta Ankara, wadda ta nemi kasar da ta bude filayen jiragen samanta da tashoshin jiragen ruwan ta ga dukkan jiragen yankin Girika na tsibirin Cyprus, wadda memba ce a cikin kungiyar EU. Shugabar gwamnatin ta Jamus ta ce tana goyon bayan warware wannan matsala kuma ta godewa Finland dangane da kokarin da ta yi na yin sulhu a lokacion shugabancinta a EU.