1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi kira ga Turkeministan da ta aiwatar canjin siyasa na zahiri

KTT ta yi kira ga gwamnatin kasar Turkeministan da ta aiwatar da canje canjen siyasa don su dace da dokokin kasa da kasa bayan rasuwar ba zata ta shugaba Saparmurat Niyazov. Shugaban kasar wanda ya mayar da kujerar mulki tamkar ta muddin rayuwa ya rasu da sanyin safiyar yau alhamis sakamakon ciwon zuciya. Yanzu haka dai an nada mukaddashin sa Gurbanguly Berdymukhammedov a matsayin shugaban rikon kwarya. A ranar talata mai zuwa majalisar koli ta kasar zata yi taro inda zata tattauna game da mutumin da zai gaji Niyazov, wanda za´a yi jana´iarsa a ranar alahadi. Ana sa ran gudanar da zaben shugaban kasa nan da watanni biyu masu zuwa.