An yi kira ga sassan dake rikici a Darfur da su ba da haɗin kai | Labarai | DW | 22.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi kira ga sassan dake rikici a Darfur da su ba da haɗin kai

MDD ta kara matsa lamba ga sassan dake rikici da juna a Sudan. A wani babban taro da ya gudamn karkashin jagorancin MDD da kungiyar tarayyar Afirka, wakilai a taron daga kasashe 26 sun yi kira ga gwamnati a birnin Khartoum da ta marawa shirin girke dakarun kiyaye zaman lafiya a lardin Darfur baya. Su kuma kungiyoyin ´yan tawaye an yi barazanar sanya musu takunkumi idan suka kauracewa taron samar da zaman lafiya da aka shirya yi a birnin Triplolis na kasar Libya a ranar 27 ga watan oktoba. To sai dai har yanzu akwai sabanin ra´ayi a dangane da hada kan rundunar kiyaye zaman lafiya ta MDD da kungiyar AU wadda zata kunshi sojoji dubu 26. Kasashen Amirka da Birtaniya na son an shigar sojojin wasu kasashe da ba na Afirka ba, amma har yanzu Sudan na adawa da haka, tana mai bukatar rundunar ta kunshi sojojin Afirka zalla.