An yi kira ga Rasha da ta daina yin katsalanda cikin kasashen makwabtanta | Labarai | DW | 04.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi kira ga Rasha da ta daina yin katsalanda cikin kasashen makwabtanta

Mataimakin shugaban Amirka Dick Cheney ya yiwa Rasha kashedi da ka da ta yi amfani da makamashi da take sayarwa kasashe ketare a matsayin wani makami na cusa musu ra´ayinta na siyasa. A lokacin da yake jawabi a gaban babban taron kasashen yankin tekun Bahar Aswad da na yankin Baltic a garin bVilnius Mr. Cheney wasu matakan da gwamnatin Rasha ke dauka ka iya kawo cikas ga dangataku tsakanin kasa da kasa. Mataimakin shugaban na Amirka ya ce bai kamata a yi amfani da man fetir ko iskar gas don aiwatar da wasu manoúfofi na danniya ba sannan sai ya kara da cewa:

“Matakan da gwamnatin Rasha ke dauke suna kawo cikas kuma zasu iya yin mummunan tasiri ga huldar dangantaku tsakanin kasashe. Ba bu doka da ta halatta yin amfani da man fetir ko iskar gas a matsayin wani makami na danniya ko yiwa wasu zagon kasa ba. Hakazalika ba wanda zai yarda da matakan yiwa ´yantattun kasashe masu ´yancin kai zagon kasa ba yi musu katsalanda a kokarin su na shimfida demukiradiya ba.”