1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi kira ga kasashe matalauta da su taimaka wajen ilmantar da matasa

September 16, 2006
https://p.dw.com/p/BujJ

A ranar farko a taron yini 5 na shekara shekara na bankin duniya da asusun ba da lamuni na duniya IMF, bankin na duniya ya yi kira ga kasashe matalauta da su kara yawan kudin da suke kashewa wajen ilmantar da matasa. A cikin wani rahoton raya kasa da ya bayar a Singapur, bankin duniya ya ce da akwai babbar fa´ida idan aka taimakawa matasa kimanin miliyan dubu 1.3. Don nuna fushi ga hana masu sukar lamirin shirin hade manufofin kasuwancin duniya wuri daya wato Globalisation halartar taron, kungiyoyi masu zaman kansu sun nesanta kansu da taron na bana. Gabanin a bude taron a Singapur ministan kudi na tarayyar Jamus Peer Steinbrück ya ce nuna bukatar dake akwai ta kulla wata yarjejeniyar ciniki tsakanin kasashen duniya.