1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi kira ga Jamusawa da su yaki ayyukan kyamar baki a cikin kasar

Kusan makonni biyu gabanin fara gasar cin kofin kwallon kafa na duniya, SGJ Angela Merkel ta yi kira ga ´yan kasar da su kara himmatuwa wajen yaki da ayyukan masu kyamar baki. Merkel ta fada a birnin Frankfurt cewar bai kamata a jurewa duk wani aiki na kaiwa baki hari ba. Ta ce ba ma kawai a lokacin gasar cin kofin kwallon kafar ba, a´a a kowane lokaci duniya na sa ido akan irin abubuwan dake wakana a cikin kasar ta Jamus. Shugaban hukumar kula da harkokin cikin gida na majalisar dokoki Sebastian Edathy yayi kira da a kara yawan ´yan sanda a gabashin kasar, inda aka fi fama da matsalar nuna wariyar launin fata. A ranakun alhamis da juma´a an kai hare hare iri dabam dabam akan baki a biranen Weimar da Berlin, inda aka yi musu rauni iri dabam dabam.