1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi kira ga Isra´ila da ta rushe katangar wariya

December 24, 2005
https://p.dw.com/p/BvFC

A lokacin da ya isa birnin Bethlehem don gudanar da bukin Kirsmati, babban bishop din majami´ar Orthodox ta masu magana da harshen Latin Michael Sabbah ya yi kira ga Isra´ila da rushe katangar nan ta wariya. Sama da mutane dubu 30 ake sa ran zasu halarci bukin addu´o´in da bishop din zai jagoranta. Masu ziyarar ibadar dai sun je birnin na Bethlehem ne, inda aka hakikance cewa a nan aka haifi Anabi Isah ASW don halartar bukin. A bana dai birnin ya ga maziyararta masu tarion fiye da a lokutan baya na lokacin bukin Kirsmati. Dukkan maziyarartan dai sun shiga Bethlehem ne daga Birnin Kudus inda a dole suka ratsa ta wani wurin bincike dake tsakanin katangar da isra´ila ta gina don hana kutsen Falasdinawa ´yan gwagwarmaya.