1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi kira ga Hamas da ta daina ta da zaune tsaye

Bayan sauyin mulki da aka samu a hukumar mulkin cin gashin kan Falasdinawa, gamaiyar kasa da kasa ta yi kira ga sabuwar gwamnatin da za´a kafa da ta amince da ´yancin wanzuwar kasar Isra´ila ba da wani sharadi ba. An bayyana haka ne yayin wata hira ta wayar tarho da aka yi tsakanin babban sakataren MDD Kofi Annan da ministocin harkokin wajen Amirka da Rasha hade da wakilan KTT. Duk da damuwar da ta nuna game da narasar da kungiyar Hamas ta samu a zaben ´yan majalisar dokoki, kungiyar EU ta ce zata ci-gaba da ba Falasdinawa taimakon kudi. To amma bisa sharadin cewa kungiyar ta masu daukar makami ta yi watsi da manufofin ta na ta da zaune tsauye kana ta shiga tattaunawa da Isra´ila tare da aiwatar da sauye sauye a cikinta. A kowace shekara EU na taimakawa Falasdinawa da kudi Euro miliyan 500. Shi kuwa a nasa bangaeren shugaba GWB na Amirka cewa yayi gwamnatinsa ba zata yi ma´amala da Hamas ba har sai ta daina kaiwa Isra´ila hare haren ta´addancin.