An yi kira ga Amirka da ta rufe sansanin Guantanamo | Labarai | DW | 19.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi kira ga Amirka da ta rufe sansanin Guantanamo

Kungiyoyin kare hakkin bil Adama sun yi maraba da rahoton da wani kwamitin MDD mai yaki da azabtar da firsinoni ya bayar, wanda ya yi Allah wadai da matakan da Amirka ke dauka na yaki da ta´adda. Lauyan kungiyar kare hakkokin jama´a a Amirka, Jamil Dakwar ya ce rahoton kwamitin bai bar wani shakku ba cewar manufofi da kuma matakan da Amirka ke dauka a cikin gida da kuma ketare sun sabawa dokokin kasa da kasa wadanda suka haramta azabtarwa da kuma cin zarafin firsinoni. Rahoton mai shafuka 11 ya yi kira ga Amirka da ta rufe kurkukunta na Guantanamo dake kasar Cuba, kana kuma ta daina amfani da sansanoni na sirri a yakin da ta ke yi da ta´adda. Rahoton ya kuma yi kira ga Amirka da ka da ta koma da firsinonin dake hannunta zuwa wasu kasashe, inda zasu iya fuskantar barazana ta azaba.