An yi kira ga Amirka da ta rufe sansanin Guantanamo dake Cuba | Labarai | DW | 11.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi kira ga Amirka da ta rufe sansanin Guantanamo dake Cuba

Babban sakataren MDD Ban Ki Monnya yi kira ga Amirka da ta rufe sansanin ta na Guantanamo dake kasar Cuba. Kiran na Ban ya zo ne a daidai lokacin da ake cika shekaru 5 da bude sansanin, inda Amirka ke tsare da muatne da ta ke zargi da aikata ta´addanci. Su ma sauran kungiyoyin kare hakkin bil Adama da shugabannin duniya baki daya sun yi kira da a rufe wannan sansani. A yau an gudanar da zanga-zanga da tarukan gangami a kasashe da dama don yin Allah wadai da sansanin. Masu zanga-zanga a birnin London sun yi amfani da wannan damar inda suka yi kira ga FM Birtaniya Tony Blair da ya taimaka a saki dukkan wadanda ake tsare da a sansanin. Amirka dai na tsare da mutane 400 a sansanin.