An yi kira da zartas da wani kuduri kan Koriya Ta Arewa | Labarai | DW | 07.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi kira da zartas da wani kuduri kan Koriya Ta Arewa

Gwamnatin Japan ta sake yin kira da a samar da wani kudurin kwamitin sulhu mai tsauri akan KTA, idan kasar ta aiwatar da aniyar ta ta gwajin makamin nukiliya. Ministan harkokin wajen Japan Taro Aso ya ce dole ne a gaggauta samun hadin kai a cikin MDD don daukar mataki na bai daya. A jiya kwamitin sulhu a birnin New York ya gargadi KTA da ka da ta yi gwajin makamin nukiliyar. Shugaban kwamtin a yanzu wato jakadan Japan a MDD Kenzo Oshima ya samu goyon bayan dukkan membobin kwamitin sulhun inda ba tare da wata hamaiya ba suka yi kira ga KTA da ta yi watsi da shirin ta na gudanar da gwajin makaman nukiliya. Bugu da kari an kuma yi kira gareta da ta koma kan teburin shawarwari na kasashe 6 game da dakatar da shirinta na nukiliya.