An yi kira da ta amince da ´yancin kasar Libanon | Labarai | DW | 03.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi kira da ta amince da ´yancin kasar Libanon

Ministan harkokin wajen Jamus F-W Steinmeier yayi kira ga Syria da ta amince da ´yancin kasar Libanon. Bayan wata ganawa da yayi da FM Libanon a birnin Beirut mista Steinmeier ya ce tattaunawar da aka shirya zai yi gobe litinin a birnin Damascus, ba ta yin sulhu ba ce, a´a ta aikewa da wani sako ne a bayyane. Ministan ya karfafa cewa Jamus zata kara yawan taimako da take bayar sannan ya jaddada cewar ziyararsa wata alama ce ta marawa gwamnatin Libanon baya. Ita ma sakatariyar harkokin wajen Birtaniya wadda ta gana da Siniora a birninBeirut ta nuna goyon baya ga FM dake fuskantar matsalolin siyasa na cikin gida. A jiya asabar ma dubun dubatan magoya bayan Syria sun gudanar da zanga-zanga a birnin Beirut na neman FM Siniora da yayi murabus. Shugaban Masar Hosni Mubarak yayi suka ga masu zanga-zangar kyamar gwamnatin ta Libanon.