An yi kira da samun cikakken hadin kan musulmi a duniya | Labarai | DW | 13.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi kira da samun cikakken hadin kan musulmi a duniya

An bude taron kolin manyan kasashen musulmi guda 8 a tsibirin Bali na kasar Indonesia, tare da yin kira da samun cikakken hadin kan musulmi baki daya. Shugaban Indonesia Susilo Bambang Yudhoyono yayi kira membobin kungiyar kasashen da ake kira Developing 8 ko kuma D-8 a takaice da su tinkari matsalar man fetir a duniya ta hanyar yin aiki tare don kirkiro da wata kafa ta samar da makamashi. Shugaban ya kuma yi kira da karfafa hadin kai don samar da kyakkyawan yanayin tuntubar juna tsakanin al´adu dabam dabam. Shi kuwa shugaban Iran Mahmud Ahmedi-Nijad wanda ya mikawa shugaba Yudhoyono shugabancin kungiyar ya yi kira ga kasashe membobin kungiyar ta D-8 da su ba juna hadin kai don inganta zamantakewa a kasashen musulmi da ma a duniya baki daya. Kungiyar ta D-8 ta kunshi kasashen Bangladesh, Masar, Indonesia, Iran, Malaysia, Nigeria, Pakistan da kuma Turkiya.