An yi kira da MDD da ta ba da umarnin janyewa dakarun ketare daga Iraƙi | Labarai | DW | 05.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi kira da MDD da ta ba da umarnin janyewa dakarun ketare daga Iraƙi

Kungiyar kasashen Larabawa ta yi kira ga kwamitin sulhun MDD da ya fitar da wani tsarin lokaci akan janyewar dukkan dakaraun waje daga Iraqi. A gun wani taro da ministocin harkokin wajen kungiyar suka yi a birnin Alkahira, sun ce dole wannan tsarin lokaci ya zama wani kuduri na MDD wanda zai ba da umarnin janyewa dakarun waje daga Iraqin. A lokaci daya kuma ministocin sun yi kira ga gwamnatin Iraqi da ta janye dukkan dokokin da ke fifita al´umomin shi´a da kurdawa. Sun kuma yi kira da a rushe dukkan kungiyoyin sojojin sa kai na shi´a a kasar. Kungiyar ta kasashen Larabawa ta ce gwamnati a Bagadaza ce alhakin warware rikici tsakanin al´umomin kasar ya rataya a wuyanta.