An yi kira da kwanciyar hankali a lokacin zaben Kongo | Labarai | DW | 29.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi kira da kwanciyar hankali a lokacin zaben Kongo

Babban sakataren MDD Kofi Annan ya yi kira ga al´umar kasar JDK da su gudanar da zaben gama gari a kasar cikin lumana ba tare da wani tashin hankali ba. A karon farko cikin shekaru 46, a gobe lahadi idan Allah Ya kaimu kasar ta Kongo zata gudanar da zaben shugaban kasa da na ´yan majalisar dokoki da ya kunshi jam´iyu barkatai. Mista Annan yayi kira ga ´yan kasar da su girmama sakamakon zaben. A jiya juma´a mutane 4, 3 daga cikin su ´yan sanda aka kashe a wata tarzoma da ta barke a wajen yakin neman zabe na daya daga cikin ´yan takara a Kinshasa babban birnin kasar. MDD da KTT sun girke sojoji kimanin dubu 19 wadanda ke taimakawa wajen samar da zaman lafiya tare da tabbatar da zaben ya gudana salin alim.