An yi kira da akwo ƙarshen rikicin siyasa a Kenya | Labarai | DW | 02.01.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi kira da akwo ƙarshen rikicin siyasa a Kenya

A dangane da munanan tashe tashen hankula dake faruwa a Kenya bayan zaɓen shugaban ƙasa da ake taƙaddama a kai, ƙasashen Amirka da Birtaniya sun yi kira ga shugabannin jam´iyun siyasa da ba sa ga maciji da juna da su nuna halin ya kamata. A cikin wata sanarwar haɗin guiwa da suka bayar, sakatariyar harkokin wajen Amirka Condoeeezza Rice da takwaranta na Birtaniya David Miliband sun ce muhimmin abu shi ne a sasanta. Mutanen biyu sun yi maraba da kiran da ƙungiyar tarayyar Afirka AU ta yi na sassan dake rikici da juna a Kenya a su kawo ƙarshen tashe tashen hankulan nan take. Ita ƙungiyar tarayyar Turai da ta ƙasashe rainon Ingila sun yi kira da a samu maslaha.