1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi kira da a magance talauci da zaman kashe wando a Afirka

May 31, 2006
https://p.dw.com/p/Buvw

Shugaban ATK Thabo Mbeki ya yi kira da a kara matsa kaimi wajen yaki da matsalolin talauci da rashin aikin yi a nahiyar Afirka. Shugaban yayi wannan kira ne a jawabin bude taron duniya kan tattalin arzikin game da Afirka dake gudana a birnin Cape Town na ATK. Shugaban ya ce idan Afirka ba ta samu wani ci-gaba a wannan fanni ba, to zata kasance nahiya daya tilo da ta kasa cimma burin MDD na ci-gaban kasashe da ake yiwa lakabi da Millenium Goals. Shi kuwa a nasa bangaren shugaban Tanzania Yakaya Kikwete ya yi kyakkyawan fata ne cewa wata bunkasa mai dorewa na taimakawa wajen rage matsalar talauci. Alkalumma dai sun yi nuni da cewa yanzu nahiyar Afirka na samun bunkasar tattalin arziki da ta kai misalin kashi 5.3 cikin 100, wadda ta kasance bunkasa mafi yawa a cikin shekaru 30. Mutane 650 daga fannonin tattalin arziki, siyasa, binciken kimiyya da kuma kungiyoyi da dama ke halartar taron, inda suke musayar ra´ayoyi kan yadda za´a samu dorewar bunkasar tattalin arziki a daidai lokacin da Afirka ke fama da matsaloli iri dabam dabam.