An yi kira da a kawo karshen rikici a arewacin Libanon | Labarai | DW | 21.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi kira da a kawo karshen rikici a arewacin Libanon

A kuma halin da ake ciki wakilin MDD a GTT Terje Roed Larsen ya nuna matukar damuwarsa game da fadan da ake yi tsakanin sojojin Libanon da masu tsattsauran ra´ayin Islama. Larsen ya yi kashedin cewa fadan ka iya rikidewa zuwa wani gagarumin yaki. Bayan wani taro da yayi da shugaban kungiyar kasashen Larabawa Amr Mussa a birnin Alkahira Larsen ya fadawa manema labarai cewa sun yi doguwar tattaunawa game da halin da ake ciki a Libanon. Ya yi kira ga dukkan wadanda abin ya shafa da su nuna halin ya kamata don gano bakin zaren warware wannan rikici.