An yi kira da a inganta halin rayuwar tsirarun kabilu a Turai | Zamantakewa | DW | 15.11.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

An yi kira da a inganta halin rayuwar tsirarun kabilu a Turai

Rayuwar tsirarun kabilu

default

Wata ´yar Roma ta na goge gilashin mota a Alabaniya

Bawa kowa dama daidaiwa daida: wannan dai shi ne taken Turai na wannan shekara ta 2007. Da haka dai KTT ta kuduri aniyar wayarwa da jama´a kai game da batun wariya. Wannan shirin dai yana da muhimmanci. Domin har yanzu da yawa daga cikin al´umomin Turai alal misali kabilar Roma ko kuma Gypsies sai dai su yi mafalkin ba su wannan dama kamar sauran tsiraru. Yawansu ya kai miliyan 12 kuma sune kabila mafi yawan mutane a tsakanin tsirarun kabilu a cikin kasashen kungiyar EU. Suna fuskantar wariya da bambamce bambamce irin dabam dabam a duk inda suke. Shirin MTK na wannan mako zai duba irin mawuyacin halin da kabilar ta Roma ke ciki. Mohammed Nasiru Auwal ke muku marhabin da saduwa da ku.

....Jingle/Musik....

Madalla. Tun daga makarantun nasare matsalolin ´yan kabilar Roma ko Gypsies ke farawa, inda ake nuna musu wariya. A saboda haka da yawa daga cikin yaran Roma ba sa zuwa wadannan makarantun. Yayin da a hannu daya iyayen su ba sa amincewa da irin wuraren a daya hannun kuwa daukacin makarantun nasaren ne ba sa daukar ´ya´yan kabilar Roma bisa tsoron cewa suna tattare da matsaloli da wahalhalu iri daban daban. Saboda haka bayan sun shiga makarantun firamare matsalolin ´ya´yan Roma na karuwa domin daukacin su yarensu suka iya wato Romanes a farkon lokacin shiga makaranta. Ba sa fahimtar abubuwan da ake koya musu a azuzuwa, tun daga sannan kuma sai su zama saniyar ware. Dole ne a gaggauta yin wani abu a dangane da wannan mawuyacin hali da ´yan Roman ke ciki, inji Kotolin Lehwo-i ´yar asalin kasar Hungary wadda kuma ta shafe shekaru masu yawa tana aikin kula da zaman jama´a musamman ´an kabilar Roma. Yanzu dai Lehwo-i ita ce mai magana da yawun ´yan social democrat masu kula da batutuwan Romawa a majalisar dokokin Turai.

1. O-Ton Levai:

“Na ga misalai kyawawa a Jamus. A can akwai wasu makarantu inda daya bayan daya ake shigar da iyayen yara baki cikin harkokin makarantu. Suna gabatar da darussan koyan harshen Jamusanci, inda iyayen da kuma yaran baki-dayan su suke koyon yaren. Hakan na bawa yaran kwarin guiwa musamman kasancewar iyayen su a kusa da su. Ga malaman ma wannan tsari na da muhimmanci domin yana ba su damar sanin iyayen yaran. Hakan dai wani ginshiki ne kwakkwara na kyautata hadin kai a gaba.”

A wasu kasashen KTT ma ana tafiyar da irin wadannan aikace aikace. To sai dai a lokuta da yawa kungiyoyi masu zaman kansu ke gabatar da wannan shiri. Yanzu haka dai kungiyar EU ta fara wasu jerin shirye shirye da nufin taimakawa ´yan kabilar ta Roma. To amma har yanzu da sauran rina a kaba inji Kotolin Lehwo-i, sannan sai ta kara da cewa.

2. O-Ton: Lehwo-i:

“Wani kyakkyawan misali shi ne, daga lokaci zuwa lokaci da ni da abokin aiki na muna kai ziyara a kasasahe daban daban, inda halin da Romawa ke ciki ya fi yin muni. Alal misali mun kai ziyara a wata cibiyar ´yan Roma dake kasar Romaniya wadda ´yan sanda suka kaiwa hari. Wannan lamari bai dauki hankali mutane sosai ba kuma in da ba mu je wurin ba to da watakila wannan rashin imanin da ´yan sandan suka yi bai baiyana a fili ba. Ina ganin ya kamata mu fadada sa ido da muke kan da nufin bayyanawa duniya mawuyacin halin da tsirarun kabilu ke ciki.”

Mafi yawa daga cikin ´yan Roma na zaune ne a kasashen gabashin Turai na kungiyar EU. A wadannan kasashen kuwa halin da suke ciki ya fi yin muni. A kasashen Hungary da Romaniya da ma Buklgariya da kuma Slovakiya akwai unguwannin ´yan Roma masu yawa, inda suke rayuwa ba wutar lantarki ba kuma tsabtattacen ruwan sha na famfo.

3. O-Ton Lehvi:

“Wadannan yankuna na fama da matsanancin talauci, to amma mutanen ba sa son yin kaura zuwa wasu wurare daban. Ba kamar a kasashe kamar Spain da Faransa ba inda tsiraru ´yan kabilar Roma ke fafatukar nemawa kansu ´yanci da walwala. ´Yan Roma a kasashen Hungary da Romaniya ba sa son yin kaura, sun fi son su ci-gaba da zama a wuraren da suke kuma a cikin halin da bai dace ga rayuwar dan Adam ba.”

A wani mataki don inganta halin da ´yan Roma ke ciki a kasashen su, kimanin shekaru biyu da suke gabata wasu kasashen gabashin Turai sun yi wata hadaka kuma tare da taimakon KTT sun tsara wani shiri na tsawon shekaru 10 da nufin karfafa shigar da ´yan Roma a harkokin yau da kullum da kyautata zamantakewa tsakanin su da sauran al´umomin kasashen da suke ciki. Hakan dai wani babban kalubale ne musamman a fannin ba da ilimi inji Kotolin Lehwo-i.

4. O-Ton Lehvi:

“Al´adun ´yan kabilar ta Roma na kawo cikas a fannoni da dama musamman a batutuwan da suka shafi mata. Alal misali suna kyamar duk macen dake sha´awar yin karatun jami´a. Sauran ´yan kasa ma ba sa amincewa da ita. Wato kenan a karshe sai ta samu kanta cikin wani hali na tsaka mai wuya. A saboda haka da yawa daga cikin matan Romawa sun fi kaunar su ci-gaba da zama a matsayin da al´adar su ta ajiye su. Zamu iya cimma wani abin kirki ne idan muka hada kai da su sannan su kuma a na su bangaren idan suka canza wasu al´adun su wadanda tuni duniya ta yi watsi su.”