An yi kira da a gudanar da taron sansanta al´umar Iraƙi | Labarai | DW | 12.08.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi kira da a gudanar da taron sansanta al´umar Iraƙi

FM Iraqi Nuri al-Maliki ya yi kira da a gudanar da wani taron koli tsakanin shugabanni siyasar kasar. Al-Maliki wanda gwamnatinsa ta shiga mawuyacin hali tun bayan ficewa ministoci ´yan sunni daga cikinta, ya ce yana sa rai shugabanni zasu tattauna akan muhimman batutuwa a dangane da siyasar kasar a gun taron wanda zai gudana nan dakwanaki kadan masu zuwa. A kuma halin da ake wani fitaccen shugaban ´yan sunni yayi kira ga kasashen larabawa da su taimaka akan abin da ya kira kungiyoyin ´yan ina ga kisa da Iran ke daurewa gindi. Adnan al-Dulaimi shugaban babban bangaren ´yan sunni a majalisar dokoki ya yi kashedin cewa Bagadaza na cikin hadarin fadawa hannun ´yan Fasha da kuma Safawi wato ´yan Iran kenan.