1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi kira da a gudanar da bincike akan kisan gillar Usbekistan a bara

May 13, 2006
https://p.dw.com/p/BuyT
Shekara daya bayan murkushe masu zanga-zanga a garin Andijan dake gabashin Osbekistan, wani gungun masu fafatukar kare hakkin dan Adam sun yi gangami a gaban ofishin jakadancin Usbekistan dake birnin Mosko. Masu zanga-zangar sun bukaci da a gudanar da bincike na kasa da kasa akan bude wutar da jami´an tsaro suka yi akan masu zanga-zangar a bara, inda aka halaka daruruwan mutane. Masu sa ido na ketare sun ce mutane fiye da 700 aka kashe amma hukumomin kasar ta Usbekistan sun ce adadin bai zarta mutum 187 ba. Masu zanga-zangar sun yi kira da gurfanad da shugaba Islam Karimov a gaban wata kotu ta kasa da kasa dangane da kisan gillar da aka yiwa masu zanga-zangar ta lumana.