1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi kira da a gaggauta girke ruduunar EUFOR a Chadi

December 9, 2007
https://p.dw.com/p/CZHl
A dangane da faɗan da ake ci-gaba da yi tsakanin ´yan tawaye da sojojin gwamnati a gabashin ƙasar Chadi, shugaban Faransa Nicolas Sarkozy na matsa lamba da a gaggauta tura dakarun ƙungiyar EU zuwa wannan yanki. A lokacin da yake magana a wurin taron ƙolin ƙungiyar EU da ta AU a birnin Lisbon, shugaba Sarkozy ya ce bai dace ba a ce an tura rundunar kasa da kasa yankin Darfur mai fama da rikici a Sudan amma a ƙasa girke wata rundunar kungiyar EU a kasar Chadi. Ya ce rikicin ya shafi yanki guda ɗaya kuma al´uma ce guda waɗanda rikicin ya rutsa da su. An yi ta dage lokacin tura sojojin rundunar EUFOR kimanin dubu 3500 da za´a girke a Chadi saboda dalilai na gudanarwa. Yanzu haka EU na fatan tura sojojin a farkon sabuwar shekara.