1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi kira da a aiwatar da canje-canje a cikin Majalisar Dinkin Duniya

Mohammad Nasiru AwalSeptember 24, 2004
https://p.dw.com/p/BvgC
Ministan harkokin wajen Jamus Joschka Fischer lokacin da yake jawabi a MDD
Ministan harkokin wajen Jamus Joschka Fischer lokacin da yake jawabi a MDDHoto: AP

Gwamnatin tarayyar Jamus na da kwararan dalilai guda biyu na neman yiwa MDD sauye-sauye. Na farko shine da tun tuni ya kamata a aiwatar da wadannan sauye-sauyen sannan biyu kuma shi ne hakan ka iya ba ta damar samun kujerar dindindin a kwamitin sulhu na MDD. Shi ya sa ba abin mamaki ba ne da ministan harkokin wajen Jamus ya karfafa bukatar dake akwai wajen yiwa MDD garambawul a lokacin jawabinsa a gaban babbar mashawartar majalisar dake birnin New York. Dukkan hujjojin da mista Fischer ya gabatar game da aiwatar da canje-canjen kuwa suna da makama, musamman ta la´akari da cewar a halin da ake ciki ba kowane yanki na wannan duniya ta mu ke da wakilci a cikin kwamitin sulhun. Alal misali kamata yayi a ba kasashen nahiyar Afirka da na yankin kudancin Amirka zaunannun kujeru a cikin kwamitin sulhun.

To sai dai har yanzu ba´a cimma manufa ba. Domin tun ba´a kai ko-ina ba wato tun ba´a gabatar da shawarwarin yiwa gamaiyar ta kasa da kasa garambawul ba har an fara wata gwagwarmaya tsakanin kasashen dake neman wannan matsayin. Alal misali kasashen 4 nan wato Jamus da Indiya da Brazil da kuma Japan na ganin sune suka fi cancanta wajen samun kujerun dindindin a kwamitin sulhu. Yanzu haka dai wadannan kasashe suna ba juna hadin kai don cimma wannan buri. Abin da akewa fargaba shine kada wasu kasashen kuma su hada kai don kalubalantar wadannan kasashe 4 don cimma wannan buri.

Sanin kowa ne cewar mallakar kujerar dindindin a kwamitin sulhu tamkar wani iko ne da angizo ga kasa. Hatta ita kanta gwamnatin tarayyar Jamus ta san da haka. Kamar sauran kasashen da ke neman kujerar dindindin a kwamitin sulhu ita ma Jamus ta kulla kawance tare da bin dukkan hanyoyin da suka wajaba don cimma wannan buri. To amma wannan matakin ka iya dakushe duk fatan da ake na yiwa MDD garambawul din da ake bukata ruwa a jallo. A karshe dai kafin a aiwatar da canje-canje dole sai an samu rinjayen kuri´u 2 bisa 3 na kasashe 191 membobin MDD da kuma amincewar dukkan kasashe 5 dake da zaunannun kujeru a kwamitin sulhu, wadanda ko da alama ba sa son su rasa wani bangare na wannan gata da suke da ita.

Abin tambaya a nan kuwa shine wani irin martani za´a mayar idan sakatare janar na MDD Kofi Annan ya gabatar da jerin shawarwari dangane da yiwa majalisar garambawul? Abin da ya fito fili a gun taron babbar mashawartar a bana shine kusan dukkan kasashen duniya ciki har da Jamus na son a yiwa Majalisar ta Dinkin Duniya kwaskwarima.