1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi kira da ɗaukar matakan yaƙi da dumamar yanayi

November 17, 2007
https://p.dw.com/p/CIRv
Babban sakataren MƊD Ban Ki Moon yayi kira ga gamaiyar ƙasa da ƙasa da ta gaggauta ɗaukar nagartattun matakan yaƙi da sauyin yanayi. Ya ce bai kamata a ƙara ɓata lokaci ba. A lokacin da yake magana yayin gabatar da rahoton ƙarshe na hukumar kula da sauyin yanayi a birnin Valencia na ƙasar Spain, mista Ban ya ce tun a babban taron MDD game da muhalli da zai gudana a tsibirin Bali cikin watan desamba ya kamata a gabatar da sahihan matakai bisa manufar tinkarar matsalar ta ɗumamar doron ƙasa. A cewar shugaban hukumar kula da muhalli ta MƊD Rajendra Pachauri, bayan shekara ta 2015, babu wani lokaci da ya saura na takaita fid da hayakin dake gurɓata doron kasa.