An yi jana´izar ´yan sandan Jamus 3 da aka halaka a Afghanistan | Labarai | DW | 18.08.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi jana´izar ´yan sandan Jamus 3 da aka halaka a Afghanistan

A yau a birnin Berlin aka yi jana´izar ´yan sandan Jamus 3 da suka rasa rayukansu a wani harin bam da aka kai kan su a Afghanistan. Ministan harkokin cikin gidan Jamus Wolfgang Schäuble ya yaba da aikin jami´an sandan na tabbatar da tsaro da samar da zaman lafiya da lumana kana kuma ya mika gaisuwar ta´aziyarsa ga iyalan su.

“Mario Keller, Jörg Ringel da Alexander Stoffels sun raya rayukansu lokacin da suke gudanar da aiki na gari na nuna jin kai. Za´a iya samun zaman lafiya da ´yanci ne idan aka tabbatar da bin doka da oda wanda zai bawa mutane kariya da kwanciyar hankali.”

Schaüble ya jaddada cewa gwamnatin tarayyar Jamus zata ci-gaba da gudanar da aikin jin kai a yankin Hindukusch. Ya ce dole Jamus ta ta sauke nauyin dake wuyan ta na yaki da ´yan ta´adda.