An yi jana´izar tsohon shugaban Chile Augusto Pinochet | Labarai | DW | 12.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi jana´izar tsohon shugaban Chile Augusto Pinochet

Tare da fareti da bukukuwa a yau sojojin kasar Chile sun nuna girmamawarsu ta karshe ga tsohon shugaban gwamnatin mulkin kama karya na kasar Augusto Pinochet wanda ya rasu ranar lahadi da ta gabata. A dangane da keta hakkin bil adama da aka yi a zamanin mulkinsa na shekaru 17, shugabar kasa Michelle Bachelet ta ki halartar gun jan´izar a yau. Maimakon haka ta aike da ministar tsaro Vivianne Blanlot don ta wakilci gwamnati. To sai dai an yi mata kuwa tare da mata tofin Allah tsine. Bayan addu´o´in da aka yi sa, an tafi da gawar tsohon shugaban kasar wani wuri inda aka kona ta.