An yi jana´izar tsofan shugaban kasar Jamus Johannes Rau a birnin Berlin | Labarai | DW | 07.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi jana´izar tsofan shugaban kasar Jamus Johannes Rau a birnin Berlin

Yau a birnin Berlin na nan Jamus, a ka yi jana´izar tsofan shugaban kasa Johannes Rau da ya rasu ranar 27 ga watan da ya gabata a yayin da ya ke da shekaru 75 a dunia.

Rau, ya rike shugabancin Jamus daga a daga 1999 zuwa shekara ta 2004.

Jawabai daban daban da aka yi a wajen jana´izar sunyi tuni da muhimmiyar rawar da ya taka, ta fanin hadin kan kasa da bunkasa tattalin arzikin ta.

A yayin da ya ke halartar taron jana´izar tsofan shugaban gwamnatin Jamus Geher Schröder, yayi kuka da hawaye,a gaban gawar mirganyi Johannes Rau.

Gerher Schröder na daya daga mutanen da su ka yi aiki kut da kut da mirganyin kasancewar a lokacin sa ne, Schröder ya rike shugabancin gwamnati.