1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi jana'izar Maragayiya Winnie Mandela

April 14, 2018

A kasar Afirka ta Kudu an yi jana'izar Maragayiya Winnie Madikizela-Mandela inda dubban mutane daga ciki da sauran kasashen suka halarta.

https://p.dw.com/p/2w3qL
Südafrika Bebgräbnis von Winnie Madikizela-Mandela in Johannesburg
Hoto: picture alliance/AP Photo/T. Hadebe

Dubban mutane a kasar Afirka ta Kudu sun halarci alhinin binne Marigayiya Winnie Madikizela-Mandela wanda aka yi a birnin Soweto, wadda ta kasance daya daga cikin wadanda suka jagoranci yaki da mulkin nuna wariyar launin fata na Turawa tsiraru, kuma da safiyar wannan Asabar aka yi addu'oi ga marigayiyar wadda take zama tsohuwar matar Marigayi Nelson Mandela bakar fata na farko da ya jagoranci kasar bayan kawo karshen mulkin nuna wariyar launin fata.

Shugaba Cyril Ramaphosa na kasar ta Afirka ta Kudu yana cikin wadanda suka nuna alhinin rasuwar Winnie Mandela wadda ake mata kirari da sunan uwar-kasa, wadda ra su kimanin makonni biyu da suka gabata. Cikin wadanda suka halarci binne marigayiyar akwai tsaffin shugabannin Afirka ta Kudu da suka hada da Thabo Mbeki, Kgalema Motlanthe gami da Jacob Zuma da manyan baki daga kasashen Afirka da sauran sassan duniya.