1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi jana´izar Janar Hajj a birnin Beirut

December 14, 2007
https://p.dw.com/p/Cbn7

An yi jana´izar babban hafsan sojin Lebanon wajen birnin Beirut a daidai lokacin da ƙasar take zaman makoki na yini guda. Da farko sai da aka kai gawar Birgadiya Janar Francois al-Hajj gidansa gabani a yi masa jana´iza. Janar ɗin da mai tsaron lafiyarsa sun rasu a wani harin bam da aka kai kan su a ranar laraba da ta gabata. A halin yanzu sojoji na binciken ko ƙungiyar al-Qaida na da hannu a wannan hari. Hajj shi ne ya jagoranci wani gagarumin farmaki da aka kai kan masu tsattsauran ra´ayin Islama a wani sansanin Falasɗinawa ´yan gudun hijira dake arewacin Lebanon a farkon wannan shekara. An so ba shi mukamin magajin babban hafsan sojin kasar Janar Michel Suleiman wanda ke kan gaba a tsakanin ´yan takarar ɗarewa kan kujerar shugaban ƙasa wadda babu kowa a kai tun bayan saukan Emile Lahoud a watan jiya.