An yi jana'izar Hans-Dietrich Genscher
April 17, 2016Talla
Kimanin mutane 800 ne suka halarci jana'izar ta Mr. Genscher da aka yi a birnin Bonn, inda aka gudanar da jawabai. Tsohon sakataren harkokin wajen Amirka George Baker na daga cikin mutanen da suka halarci wannan taro. Hans-Dietrich Genscher dai ya shafe shekaru 18 a matsayin ministan harkokin wajen Jamus kuma ya taka muhimmiyar rawa wajen haɗewar Jamus ta Gabas da ta Yamma a matsayin kasa guda. Hans-Dietrich Genscher dai ya rasu ya na da shekaru 89 a ranar biyu ga watan Afrilu. Ya rasu ya bar mai dakinsa Barbara da yara da kuma jikoki da dama.