1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi hawan Arafat yau a kasa mai tsarki

December 29, 2006
https://p.dw.com/p/BuW2

Sama da musulmi miliyan biyu dake aikin Hajjin bana sun yi hawan Arafat yau a kusa da birnin Makka, inda suka yi addu´o´i ga musulmi a ko-ina cikin duniya tare da fatan kammala aikin Hajjin lamun lafiya. Musulmi dai sun yi imanin cewa Allah SWT na amsa addu´o´insu kai tsaye idan suka tsaya a wani wuri mai tsarki dake kan farfajiyar dutsin Arafat, inda Annabi Mohammed SAW ya yi hudubar sa ta bankwana kimanin shekaru dubu 1 da 400 da suka wuce. A cikin harami don nuna dukkan musulmi daya ya ke da dan´uwansa musulmi, tun da sanyi safiyar yau mahajjatan sun ka yi tattaki zuwa Jebel-al Rahman wato Tsaunin Rahma suna masu amsa kirar Ubangiji.