1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi hasashen cewa shugaba Chavez zai lashe zaben Venezuela

A kasar Venezuela ma a yau ake gudanar da zaben shugaban kasa, inda binciken jin ra´ayin masu zabe ya nunar da cewa shugaba mai ci Hugo Chavez zai lashe wannan zabe da gagarumar nasara. Rahotanni sun tabbatar da cewa babban abokin adawa kuma dan ra´ayin mazan jiya, Manuel Rosales ba zai kai labari ba a zaben na yau. To sai dai a hira da radiyon DW ya yi da shi mista Rosales ya ce kasar ta Venezuela na fuskantar hadarin komawa wata kasa ta shugaba dan kama karya har in aka sake zaban Chavez. Shi kuwa shugaban na zargin ´yan adawa ne da kokarin haddasa rudami a cikin kasar.