An yi harbe-harbe a filin jiragen sama na Turkiya | Labarai | DW | 06.11.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi harbe-harbe a filin jiragen sama na Turkiya

Wani mutumin ya sa 'yan sanda suka firgita bayan da suka tsaidashi ya ki tsayawa.

Hukumomi a Turkiya sun rufe filin jiragen sama na Atatürk da ke a birnin Santanbul ba shiga ba fita. Bayan da 'yan sanda suka bude wuta a lokacin da aka tsaida wani mai babur ya ki tsayawa, kafin daga bisanin 'yan sanda su bi mutmunin su damke shi ba tare da kowa daga ciki ya samu rauni ba.

A cikin watan Yuni da ya gabata a wani harin da kungiyar IS ta kai a filin jiragen saman na Atatürk mutane 41 suka mutu kana wasu 239 suka jikkata.