An yi garkuwa da wata Bajamushiya ´yar agaji a birnin Kabul | Labarai | DW | 18.08.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi garkuwa da wata Bajamushiya ´yar agaji a birnin Kabul

Akalla mutane 15 aka kashe sannan aka jikata wasu 25 a wani harin kunar bakin wake da aka kai a kudancin Afghansitan. Daukacin wadanda suka rasu fararen hula dake aiki a wani kamfanin tabbatar da tsaro na Amirka dake kare ayarin motoci sojin Amirka a ciki da kewayen Kandahar. A yau dai a birnin Kabul wasu ´yan bindiga sun yi garkuwa da wata Bajamushiya shugabar ofishin kungiyar agaji ta Ora International. A halin da ake ciki ma´aikatar harkokin wajen Jamus a birnin Berlin ta kafa wani kwamiti dake duba wannan batu. Kungiyar Taliban ta ce babu ruwan ta da wannan garkuwar. A wani labarin kuma kakakin Taliban ya ce ba´a cimma tudun dafawa ba a tattaunawar da ake da nufin sako sauran ´yan KTK 19. Yace yanzu haka kungiyar ta ´yan Takifen na tunanin irin mataki da zata dauka nan gaba dangane da makomar mutanen. Gwamnatin Afghanistan dai ta ki mika kai ga bukatun ´yan Taliban.