An yi garkuwa da wasu yan ƙasar China guda 7 a ƙasar Kamaru | Labarai | DW | 13.03.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi garkuwa da wasu yan ƙasar China guda 7 a ƙasar Kamaru

Wasu waɗanda ba san ko su wanene ba sun yi garkuwa da wasu yan ƙasar China 7 a ƙasar Kamaru

default

Tutar ƙasar Kamaru

Wasu majojiyoyi daga ƙasar Kamaru sun ce an sace wasu 'yan ƙasar China guda 7 aka kuma yi garkuwa da su a yankin Bakasi dake a kudu maso yammaci ƙasar. Kanfanin dillanci labarai na Faransa AFP da ya ambato cewa har yanzu ba a san ko su wanene ba ke garkuwa da mutane, ya ce ana kyautata zaton cewa 'yan ƙungiyar Afrika Marine Komando AMC, sune suka yi awan gaba da 'yan ƙasar Ta China da suka kame tun ran Juma'a. Yankin dai na Bakasi na ƙasar ta Kamaru mai arzikin man fetir da gas ya koma hannu ƙasar ta Kamaru ne, a shekara ta 2008 bayan rikicin kan iyakar da aka yi kusan shekaru 15 ana yi   akan yankin, tsakanin Nageria da Kamarun.

Mawallafi: Abdurahman Hassane

Edita: Mohamed Nassiru Awal