An yi garkuwa da wasu Faransawa ’yan yawon shaƙatawa guda 4 a ƙasar Yemen. | Labarai | DW | 10.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi garkuwa da wasu Faransawa ’yan yawon shaƙatawa guda 4 a ƙasar Yemen.

Rahotannin da ke iso mana daga Yemen sun ce wasu mutane daga gungun ’yan ƙabliun ƙasar sun yi garkuwa da ’yan yawon shaƙatawa, Faransawa, guda 4 a gabashin ƙasar, don neman cim ma sako ’yan ’uwansu da ke ɗaure a kurkuku. Jami’an ƙasashen Yemen ɗin da Faransa dai sun ce suna bai wa juna haɗin kai wajen cim ma sako ’yan yawon shaƙatawar. A cikin ’yan shekarun da suka wuce dai, ’yan ƙabilu sun sha yin garkuwa da ’yan yawon shaƙatawa da baƙi masu aiki a Yemen ɗin, don neman a gina musu ingantattun makarantu, da hanyoyi da ababan jin daɗin rayuwa ko kuma don sako ’yan uwansu da ke ɗaure a gidajen yari. Wata majiyar tsaro ta Yemen ɗin ta ce ’yan ƙabilun da suka yi garkuwa da wasu Jamusawa a shekarar bara ne suka sake yin garkuwa da Faransawan a wannan karon. Shugaban ƙasar Yemen Ali Abdullahi Saleh ya lashi takobin fatatttakar duk wasu masu garkuwa da mutane a ƙasarsa.